Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Tuesday, May 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiZamu kawo ƙarshen wahalar man fetur gobe laraba- NNPCL.

Zamu kawo ƙarshen wahalar man fetur gobe laraba- NNPCL.

Date:

Kamfanin mai na kasa, ya tabbatar da cewa, gobe Laraba za a kawo karshen wahalar da ake fama da ita ta karancin mai, da ta haddasa tashin farashinsa a ko ina a Nijeriya.

Babban jami’in harkokin sadarwa na kamfanin, Olufemi Soneye, ya shaidawa manema labarai yau a Lagos cewa, yanzun haka akwai mai da yawansa ya zarta lita milyan dubu da dari biyar, da zai wadaci bukatar al’umma ta tsawon wata guda, saboda haka zuwa gobe, dukkan wani dogon layin abubuwan hawa a gidajen mai zai kau.

Ya kara da cewa, abun takaici ne ganin yadda wasu mutane ke fakewa da yanayin da ake ciki na karancin man suna azurta kansu.

Haka-zalika, shi ma mataimakin shugaban kungiyar dilllalan mai ta kasa, Hammed Fashola, ya bayyana yakinin da yake da shi cewa, a wannan mako za a kawo karshen matsalar karancin man a jihohin Lagos da Ogun, amma watakila, a ci gaba da ganin dogon layi a birnin tarayya Abuja, saboda nisan da garin yake da Lagos.

Latest stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...

Related stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...