Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKotu ta ɗage shari'ar zargin tsohon gwamna Ganduje.

Kotu ta ɗage shari’ar zargin tsohon gwamna Ganduje.

Date:

Babbar kotun jihar Kano ta dage shari’ar zargin tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje da iyalansa da wasu makusantansa da cin hanci da karkatar da kadarorin gwamnati.
Alkalin kotun, mai Shari’a Usman Na’abba, ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Mayun gobe, bayan sauraron bangarorin dake shari’ar kan bukatar mikawa wadanda ake zargi sammaci, ba gaba da gaba ba.
Bayan zaman na yau Litinin, lauyan gwamnatin Kano dake karar su Ganduje, Barista Usman Umar Fari, ya bayyana cewa a zama na gaba ne alkali zai bayyana matsayarsa bayan sauraron jawabin bangarorin.
Idan za a iya tunawa dai, kotun ta gaza zamanta na farko ranar 17 ga watan Aprilu, saboda gazawar bangaren gwamnati wajen bai wa wadanda ake kara takardar sammaci.
Lauyan ya bayyana cewa, a kan haka ne alkali ya saurari hujjojin bangarorin biyu kan halasci ko haramcin mika sammaci ga wanda ake kara a shari’ar tuhuma, ba kai-tsaye ba.
A cewarsa, bangarensu sun bayyana wa alkali hujjojin da suke ganin ya halasta a bisa doka a mika wa wanda ake zargi a irin wannan shari’a sammaci ba kai tsaye ba, amma bangaren wadanda ake kara sun soke hakan.
Gwamnatin Kano ce dai, ta hannun hukumar yaki da rashawa ta jihar ke zargin gwamantin Ganduje da karkatar da kudaden kananan hukumomi da wasu makudan kudade hadi da kadarorin gwamnati.

 

Latest stories

Related stories