Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Tuesday, May 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiA mahaifata sai da izinin ƴan bindiga muke noma-Attahiru Bafarawa.

A mahaifata sai da izinin ƴan bindiga muke noma-Attahiru Bafarawa.

Date:

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya koka da cewa sai al’ummar mahaifarsa sun nemi izinin yan bindiga suke iya noma gonakinsu.

Ya shaidawa yan jarida a yau cewa, shi kansa dole ya hakura da noma gonarsa mai fadin kadada dubu 10 saboda rashin tsaro.

Da yake magana a kan tsadar kayan abinci, Bafarawa ya danganta matsalar da rashin tsaro, yana mai cewa yan bindiga ne ke zabar gonakin da ake nomawa a mahaifarsa da ke karamar hukumar Isa.

Ya ce a Bafarawa matsalar tsaro ce ta kawo tsadar kayan masarufi saboda manoma ba sa iya zuwa su noma gonakinsu.

Ya kara da cewa a baya ya taba jan hankalin gwamnati game da yiwuwar tashin farashin kayan abinci saboda wannan matsalar amma suka ki sauraron shawarar.

Bafarawa ya bayar da shawarar hadin kai tsakakin gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi wajen magance matsalar tsaro, musamman a yankin Arewa, saboda a cewarsa gwamnatocin jihohi kadai ba za su iya ba sai da taimakon gwamnatin tarayya.

Ya kuma yi kira ga shugabanni da su farka daga barcinsu domin magance matsalar kafin ta gagari kundila.

Latest stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...

Related stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...