Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Thursday, May 16, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiRiƙaƙƙen dillalin kwaya da aka daɗe ana nema ya shiga hannu.

Riƙaƙƙen dillalin kwaya da aka daɗe ana nema ya shiga hannu.

Date:

Rundunar yansandan jihar Kano ta ce ta kama wani riƙaƙƙen dillalin kwaya da ta daɗe tana nema ruwa a jallo tare da wasu mutum takwas.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a yau Litinin, ta ce sun yi nasarar kama Sadam Mu’azu, wanda aka fi sani da Badoo, bayan ƙorafe-ƙorafen da mazauna unguwar Takuntawa suka kai mata.

Ta ƙara da cewa dakaru sun kama ƙarin mutum takwas daga cikin yan tawagar matashin mai shekara 33, waɗanda ke samun tabar wiwi daga kudancin ƙasar nan kuma yake rarraba wa mutane har da matan aure a gidaje.

Rundunar ta ce ta ƙwace ƙunshi 11 na abin da take zargin tabar wiwi ce da gatari da babura biyar da ake amfani da su wajen rarraba kayan da kuma kuɗi Naira dubu 111 da 500 da ga hannunsu.

Ta ce za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...