Saurari premier Radio
34.5 C
Kano
Thursday, May 16, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiƘungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Date:

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar Hamas ta isa birnin Al’Qahira, yayin da aka sake farfado da zaman tattaunawa domin tsagaita wuta a hare-haren da sojojin Isra’ila ke kaiwa Falasdinawa a yankin Gaza.

An tabbbatar da cewa, jami’an Hamas uku da suka taso daga birnin Doha a kasar Qatar, sun sauka a jirgin sama domin tattaunawa da sauran wakilai masu ruwa-da-tsaki dangane da yadda za’a yi musayar Falasdinawa fursunoni da ke gidajen Yarin Isra’ila, da Yahudawan da aka yi garkuwa dasu ranar 7 ga watyan Oktobar bara.

Wata kafar labaran Isra’ila ta ce Shirin da ke hannu shi ne na musayar mutane 33 da Hamas ke garkuwa dasu, da daruruwan fursunonin Falasdinawa, da suka hada da tsofaffi, da sojoji mata, da masu tabin hankali.

Karkashin wannan yarjejeniya, tilas ne kuma Isra’ila ta janye sojojinta daga kan wata babbar hanya da ta raba zirin Gaza gida biyu.

Yanzun haka dai mafi rinjayen mazauna wannan yanki sun tsere zuwa kudancin Gaza daga arewa domin tsira da rayukansu.

Sai dai kuma tana-kasa-tana-dabo, domin masu sharhi na ganin tilas Firaminista Benjamin Netanyahu ya zabi abu daya, tsakanin musayar wadanda Hamas ke rike dasu, da dorewar gwamnatinsa.

Latest stories

Hajjin Bana: Yau Laraba za a fara jigilar alhazan kasar nan zuwa Saudiyya

Mukhtar Yahya Usman A yau Laraba ake sa ran fara...

Sheik Abduljabbar Kabara ya sake korar Lauyansa.

Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da aka yanke wa hukuncin...

Related stories

Hajjin Bana: Yau Laraba za a fara jigilar alhazan kasar nan zuwa Saudiyya

Mukhtar Yahya Usman A yau Laraba ake sa ran fara...

Sheik Abduljabbar Kabara ya sake korar Lauyansa.

Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da aka yanke wa hukuncin...