Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHajjin Bana: Yau Laraba za a fara jigilar alhazan kasar nan zuwa...

Hajjin Bana: Yau Laraba za a fara jigilar alhazan kasar nan zuwa Saudiyya

Date:

Mukhtar Yahya Usman

A yau Laraba ake sa ran fara jigilar Alhazan Najeriya zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2024, inda za a kaddamar da jirgin farko a jihar Kebbi.

Kimanin alhazai fiye da dubu hamsin ne ake sa ran za su gudanar da aikin hajjin na bana a kasar Makka da ga Najeriya.

Ayarin farko na alhazan Najeriya tuni suka hallara a sansanin alhazai da ke Birnin Kebbi inda suke jiran a kwashe su zuwa Saudiyya.

Su ma Jami’an hukumar jin dadin alhazai ta kasa tuni su ka isa Birnin Kebbi domin kaddamar da tashin jirgin farko da zai dauki alhazan.

Tun da farko dai hukumar alhazan Najeriya ta bayyana cewa, kamfanonin jiragen saman Air peace, Max Air da Saudi airlines da na Flynas a matsayin wadanda za su yi aikin kai alhazan Najeriya zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2024.

Kamfanin Flynas ne ake sa ran zai dauki alhazan na jihar Kebbi a ranar Laraban nan.

Sauran jihohin da kamfanin na Flynas zai yi jigilar su zuwa kasar ta Saudiyya sun hada da jihohin Ikko (Lagos), Osun, Ogun, Borno, Niger, Sokoto, Yobe da Zamfara.

Shugaban Hukumar alhazan ta Najeriya NAHCON, Malam Ahmad Jalal Arabi, ya tabbatar da cewa, Hukumar ta shirya tsaf wajen tabbatar da ganin an kwashe alhazan kasar baki daya zuwa kasa mai tsarki, da kuma dawo da su gida akan lokaci bayan kammala aikin hajjin.

 

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...