Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSiyasa"Baka ci zabe ba"-Martanin INEC ga AA | Premier Radio | 12.04.2023

“Baka ci zabe ba”-Martanin INEC ga AA | Premier Radio | 12.04.2023

Date:

Hukumar zaɓe Mai Zaman Kanta ta kasa INEC ta mayar da martani kan ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar dangane da korafin da yake kan sakamakon zabe.

INEC ta ce Atiku Abubakar ya gaza cika sharuɗan da kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada kafin a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.

Hukumar ta ce Atiku ya gaza samun kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a aƙalla kashi biyu bisa uku na jihohin ƙasar 36 da kuma birnin tarayya Abuja, wanda hakan na daga cikin sharuɗan cin zaɓe a ƙasar.

Hukumar Zaben ta kuma buƙaci kotun sauraron kararrakin zabe da ta yi watsi da ƙorafin da ɗan takarar ya shigar gabanta, yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC nasara.INEC

Latest stories

Related stories