Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShariah da KotuKotu: Gawuna bai shiga sahun karar da APC ta shigar ba |...

Kotu: Gawuna bai shiga sahun karar da APC ta shigar ba | Premier Radio | 12.04.2023

Date:

Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta shigar da INEC kara gaban kotun sauraron shari’o’in zabe, tana mai kalubalantar nasarar Abba Kabir Yusif na NNPP a zaben 18 ga watan Maris.

APC tace Abba bai cancanci yin takara a zaben ba, sabida babu sunansa cikin mambobin NNPP da aka aikewa INEC.

Wadanda ake karar sun hada da Abba Kabir Yusif, NNPP da kuma hukumar zabe INEC.

To sai dai, dan takarar gwamna a APCn, Dr Nasiru Yusuf Gawuna, baya daga cikin masu karar, kasancewar tun a baya ya sanar da karbar kaddara.

Jam’iyyar ta APC ta kuma yi zargin cewa NNPP bata sami kuri’u mafi rinjaye a zaben da aka gudanar ba, sabida yawancin kuri’un da aka kada musu sun lalace, idan kuma aka cire su, to APC ce zata dawo sama.

Ta roki kotun da ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, wato inconclusive, sabida ratar kuri’un da suka baiwa Abba nasara, basu zarta yawan wadanda aka lalata ba.

Wadanda ake karar na da kwanaki 21 don amsa wannan kalubale da zarar kotu ta kammala duba bukatun.

 

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories