Saurari premier Radio
34.3 C
Kano
Monday, September 25, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnatin Kano: Rabon tallafin kayan sallah | Premier Radio | 19.04.2023

Gwamnatin Kano: Rabon tallafin kayan sallah | Premier Radio | 19.04.2023

Date:

Ma’aikatar harkokin mata da ci gaban jama’a ta jihar Kano ta raba sabbin tufafi ga kananan yara a jihar.

Kwamishiniyar harkokin mata Dr Zahra’u Muhammad-Umar ta bayyana hakan ne a lokacin da take rabon kayan a Kano a ranar Talata.

Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da mazauna gidan gyaran hali, gidan yara na Nassarawa, da kuma gidan gyaran hali na Goron Dutse.

Kayayyakin da aka raba sun hada da sabbin tufafi, takalma, belts, kayan ado da kayan kwalliya.

ta ce an yi hakan ne don sanya yaran su ji ana son su kamar sauran yara tare da sanya farin ciki a fuskokinsu.

Da take jawabi a madadin jami’an da ke kula da gidajen, Hajiya A’isha Sani-Kurawa, ta yabawa gwamnatin jihar kan yadda ta ke kokari akan yaran.

Latest stories

Related stories