Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiINEC zata gurfanar da masu laifin zabe 200 a gaban kotu

INEC zata gurfanar da masu laifin zabe 200 a gaban kotu

Date:

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC zata gurfanar da mutane sama da 200 da aka kama bisa laifuka daban-daban na zabe a yayin babban zaben 2023 da aka kammala.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan bayan kammala bincike ta mika wasu kararraki sama da 50 na laifukan zabe ga hukumar zaben.

Babban sakataren yada labarai na shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya shaida wa jaridar PUNCH a wata hira ta musamman cewa, “Hukumar ta karbi takardun kararraki sama da 50 daga hukumomin ‘yan sanda. Akwai sama da mutane 200 da ake tuhuma da za a gurfanar da su gaban kuliya.

“Hukumar ta umurci sashen shari’ar na INEC da ya yi nazarin bayanan tare da ba ta shawara a kan gabatar da kara. Tuni dai sashen ya fara aiki kuma da zarar ya kammala zai bada cikakken rahoto ga shugabancin hukumar.”

Idan za’a iya tunawa a ranar 13 ga Maris, 2023, Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya umurci kwamishinonin ‘yan sandan da su tabbatar da gudanar da bincike a kan duk wani abu da ya saba wa dokar zabe a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na ranar 25 ga Fabrairu, 2023.

A ranar 14 ga watan Maris, Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar ta kafa wata tawagar lauyoyi da za ta tunkari wadanda suka karya dokar zabe a zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...