Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSarkin Musulmi Ya Bukaci A Fara Duban Jinjirin Watan Karamar Sallah.

Sarkin Musulmi Ya Bukaci A Fara Duban Jinjirin Watan Karamar Sallah.

Date:

Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na 3, ya bukaci al’ummar musulmi a fadin kasar nan da su fara neman jinjirin watan Shawwal daga gobe Alhamis.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan gudanarwa majalisar majalisar koli kan harkokin addinin musulunci ta kasa, Zubairu Haruna Usman Ugwu, ya fitar yau.

Sarkin wanda shi ne shugaban majalisar kolin, ya ce sakamakon shawarar da kwamitin ganin wata na kasa ya bayar, ya umarci al’ummar musulmin Najeriya da su nemi jinjirin watan Shawwal bayan faduwar rana a gobe Alhamis 29 ga Ramadan 1444, wanda ya yi daidai da 20 ga Afrilun 2023.

Ya ce idan ba a ga jinjirin watan a goben ba, to Asabar 22 ga Afrilu, ta zama ranar Idin karamar sallah.

Ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da shugabannin addinin Musulunci da na gargajiya a kowace karamar hukuma, da su tuntubi yan kwamitin ganin wata domin kai rahoton ganin jinjirin watan Shawwal din.

Latest stories

Related stories