Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Monday, May 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZaben Adawama: Tinubu ya bukaci jami’an tsaro su yi bincike

Zaben Adawama: Tinubu ya bukaci jami’an tsaro su yi bincike

Date:

Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bukaci rundunar yan sandan ta yi cikakken bincike kan abin da ya faru a zaben gwamna a jihar Adamawa.

A wata sanarwa da ya fitar, Tinubu ya bukaci zababbun ‘yan siyasa da su sadaukar da kansu ga ayyukan al’umma.

Tinubu ya ce ya lura da abubuwan da suka faru a zaben gwamnan jihar Adamawa ya kasance abun kunya ga kasar nan, don haka ne ya yi kira ga hukumar ‘yan sanda da ta yi cikakken bincike kan duk abin da ya faru a zaben ganin yadda aka samu sabani a yayin tattara sakamakon.

Ya ce a kowace takara ta dimokuradiyya dole ne a samu nasara guda daya, saboda haka ya yi kira ga wadanda abin ya shafa da su bi hanyoyin da suka dace don magance korafe-korafe.

Tinubu ya kuma yi kira ga daukacin wadanda aka zaba a zaben 2023 da su jajirce wajen gudanar da aikin da ke gabansu da kuma shirya yiwa al’umma hidima.

 

Latest stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...

Related stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...