Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeShirye-shiryeHira ta MusammanYadda dan majalisa ya kama wanda ya kayar da shi a zabe...

Yadda dan majalisa ya kama wanda ya kayar da shi a zabe | Premier Radio | 26.03.2023

Date:

Zababben dan majalisar dokokin jihar Yobe, Lawal Musa Majakura, yayi Karin bayani kan yadda abokin takararsa, dan majalisa mai ci Ahmed Mirwa ya daure shi, bisa zargin kalubalantar wakilcin sa.

 

Mirwa, wanda shine kakakin majalisar dokokin Yobe, ya sha kayi a hannun Majakura, matashi dan shekaru 34, a zaben da ya gudana a rana 18 ga watan Maris, bayan shafe sama da shekaru 20 yana wakilcin mazabar Guru II a jihar.

 

Alkaluman zaben sun nuna cewa Majakura ya yi nasara ne da tazarar kuri’u 182 tsakaninsa da Mirwa.

 

Matashin, wanda yayi takara a karkashin jam’iyyar PDP, ya shaidawa Jaridar DailyTrust ta wayar talho yadda lamarin ya kasance.

 

“Sau biyu ana kama ni. Na farko wani dan siyasa ne a APC, tun kafin na fice daga jam’iyyar, bayan na wallafa wani sako a Facbook ina kalubalantarsa. Shine ya sa yan sanda suka tsare ni tsawon kwanaki 5”. Inji Majakura.

 

“Na biyun, shugaban majalisar dokokin ne, wanda na kayar a zabe.  Ya sanya an tsare ni sabida na kalubalanci wakilcinsa, an tsare ni na tsawon kwanaki 2. Tun a watan Azumin bara”.

 

Ya kara da cewa dalilin kamashin, ba zai wuce yadda yake bibiyar ayyukan yan majalisar ba, inda yakan bi sahun ayyukan mazabu da gwamnatin jihar ke sahalewa yan majalisa, tare da fallasa duk wani zargi na rashin adalci.

 

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories