Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTinubu ya musanta ganawa da babban jojin kasarnan a london

Tinubu ya musanta ganawa da babban jojin kasarnan a london

Date:

Zaɓabben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya musanta rahotannin da ke cewa ya gana da babban jojin kasar nan a birnin London.

Wata sanarwa da ta samu sa hannun daraktan yaɗa labaru na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bayo Onanuga, ta bayyana labarin a matsayin ƙage maras tushe.

A cikin kwanakin nan ne wasu jaridu da kuma masu amfani da shafukan sada zumunta suka rinka yaɗa labarin yadda aka yi wata ganawar sirri, tsakanin Bola Ahmed Tinubu da babban jojin Najeriya, Olukayode Ariwoola.

Labarin ya nuna cewa babban jojin ya yi ɓadda-bami ta hanyar hawa keken guragu domin ganawa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a birnin London.

Sai dai sanarwar, wadda aka fitar ta ce an ƙirƙiri labarin ne domin sanya shakku a zukatan ƴan Najeriya game da nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaɓen da ya gabata.

A cikin sanarwar, Mr Onanuga ya ce yanzu haka Bola Tinubu, wanda ya bar Najeriya a ranar Talatar da ta gabata , yana a ƙasar Faransa, inda yake hutawa domin sauke gajiyar yaƙin neman zaɓe.

Sai dai ya ce Tinubun zai isa birnin London ne nan gaba, kafin ya tafi Saudiyya domin yin Umara.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...