Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSarkin Bichi ya kadamar da tashar wutar lantarki mai amfani da hasken...

Sarkin Bichi ya kadamar da tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana

Date:

Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero ya jagoranci bikin kaddamar da tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana wanda kamfanin Sandstream Nigeria limited hadin gwiwa da majalisar masarautar Bichi suka samar a garin Yallami dake karamar hukumar Bichi.

Mai martaba Sarkin ya yabawa kokarin kamfanin na samar da wannan aiki, inda yace hakan zai taimakawa al’umma duba da yadda ake fuskantar karancin wutar.

Ya kuma ja hankalin jama’ar garin dasu kula da kayayyakin da kuma kula da tashar domin ganin bata gari basu lalata ba.

A jawabinsa Shugaban Kamfanin na Standstream Nigeria Limited Alh Ibrahim yace wutar za’a hadata a gidaje da kuma Shaguna dake garin na Yallami domin inganta kasuwanci a yankin.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories