Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnatin Kano ta gamsu da tsaftar muhallin Kanawa

Gwamnatin Kano ta gamsu da tsaftar muhallin Kanawa

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta nuna gamsuwar ta da yadda al’ummar jihar Kano ke cigaba da baiwa aikin tsaftar muhalli na kowa da kowa hadin kan daya kamata.

Kwaminishinan ma’aikatar muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana haka jim kadan bayan jagorantar aikin tsaftar muhalli na karshen wata wata wanda ya gudana a wannan rana.

Ya kara da cewa, gwamnatin jihar Kano tana bakin kokarin ta wajan ganin jihar nan ta cigaba da rike matsayin ta na wacce tafi ko wacce jiha tsaftace muhalli.

Dakta Kabiru Getso yace al’umma sun zauna a gidajen su domin shiga cikin aikin tsaftar muhallin a yau Asabar duk da cewar wasu daga cikin matuka babura masu kafa sun gudanar da zirga zirga a lokacin aikin tsaftar muhallin.

Daga bisani Dakta Kabiru Ibrahim Getso, ya tabbatar da cewa daga cikin wadanda suka gudanar da zirga zirga a lokacin aikin tsaftar muhallin masu shari’a dake kwaminitin aikin tsaftar muhalli na karshen wata wata sun zartar musu da hukuncin laifin da suka aikata.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...