Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShariah da KotuZaben 2023: An shigar da kararraki sama da 100 | Premier Radio...

Zaben 2023: An shigar da kararraki sama da 100 | Premier Radio | 26.03.2023

Date:

Hukumar zabe INEC ta yi kasafin kudi sama da naira biliyan 3 domin tunkarar shari’o’in zaben shugaban kasa, gwamnoni da na yan majalisa, wadanda aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabarairu, da 18 ga watan Maris din 2023.

Yan takarar kujeru daban daban da suka sha kayi, sun shigar da kara a kotu, domin kalubalantar sakamakon zaben.

Zuwa yanzu, sama da kararrakin zaben 100 aka shigar gaban kotu, daga yan siyasa a sassan Najeriya.

Jam’iyyun da suka shigar da kara akan zaben shugaban kasa sun hada da PDP, LP, AA, APM da sai sauransu.

Har ila yau, an sami bore daga wasu jam’iyyu kan rashin gamsuwa da zabukan yan majalisa da gwamnoni.

Hatta a jihar Kano, jam’iyyar APC mai mulki, wadda ta sha kayi a zaben gwamna, ta gudanar da zanga zangar lumana domin kalubalantar zaben.

A watan Nuwambar 2022, shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya koka kan yadda shari’o’in zabe sama da 600 suka yiwa hukumar katutu.

Da yake jawabi a wani taron karawa juna sani a aka shiryawa alkalai sama 300, wadanda zasu tunkari shari’un, Mahmood ya shaida cewa yawancin shari’o’in dake gaban INEC sun shafi na zabukan cikin gida ne.

Zuwa yanzu, babu wani Karin bayani kan adadin lauyoyin da hukumar ta shirya dauka domin kare kanta.

 

Latest stories

Related stories