Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaMajalisa: Kudirin haramtawa likitocin Najeriya aiki a waje | Premier Radio |...

Majalisa: Kudirin haramtawa likitocin Najeriya aiki a waje | Premier Radio | 07.04.2023

Date:

Wani kudirin doka da zai hana likitocin Najeriya ficewa daga kasar har sai sun yi aikin tsawon shekaru 5 a cikin gida, ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai.

Manufar dokar itace dakile karuwar adadin likitocin dake ficewa aiki waje, bisa kwadaituwa da kyakkyawan yanayi.

Mamba a majalisar, Ganiyu Abiodun Johnson ne ya dauki nauyin kudirin, wanda aka yi wa take da ‘kudirin yiwa dokar likitoci ta 2004 kwaskwarima’.

Johnson yace zai fi kyautuwa likitocin su fara amfanar da cikin gida da kwarewar da suka samu karkashin kulawar kasa, akalla da shekaru 5 kafin su fice.

Zaman majalisar na ranar Alhamis, 6 ga watan Aprilu, karkashin jagorancin Femi Gbajabiamila ya amince da wannan kudiri a karatu na biyu.

 

 

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories