Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Monday, May 6, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaZa'a fuskanci tsananin zafi a wasu jihohin Arewa - NIMet

Za’a fuskanci tsananin zafi a wasu jihohin Arewa – NIMet

Date:

Hukumar Kula da Yanayi ta kasa (NiMet) ta gargadi mazauna Abuja, Kano, da Kogi da wasu jihohin Arewa da dama, game da tsananin zafin da za’a fuskanta na tsawon kwanaki uku da zai fara daga yau Asabar.

Tsananin zafin da zai Kai ga illata jiki da Suma da matsala karancin ruwa a jikin alumma.

Rahoton ya tabbatar da Jihohi irin su Abuja, Kano, Sokoto, da Kogi zasu fuskanci tsananin hadarin matsanancin zafin Inda hukumar ta bukaci mazauna yankin su dauki matakan riga-kafi cikin gaggawa don rage barazanar kamuwa da cutuka masu alaka da zafi da suka hada da shanyewar jiki.

NIMet ta shawarci Alumma su tsananata Sha ruwa mai yawa, su kunna naurar sanyaya daki, su guji rufe Yara a cikin mota mai zafi, su zauna a cikin gida musamman da tsakanin karfe shabiyun rana zuwa karfe hudun yamma, idan fitar waje ya zama dole ayi kokarin rufe Kai da hula saboda rage zafin ranar.

Hakazalika a tabbatar da bawa yara isasshen ruwan sha don gujewa kamuwa da cutuka masu alaka da zafin.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...