Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Monday, April 29, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiIdan aka inganta ayyukan Sojoji za su magance matsalar tsaro a Najeriya...

Idan aka inganta ayyukan Sojoji za su magance matsalar tsaro a Najeriya – Kwankaso

Date:

Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce sojoji zasu iya kawo karshen matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta.

Kwankwaso ya bayyana hakane yayin ganawa da manema labarai bayan taron kwamitin zartaswa na jam’iyar NNPP a Abuja.

Ya ce duk da cewa hakkin gwamnatin tarayya ne ta magance matsalar tsaro, saidai ‘yan Najeriya suna da rawar takawa ta hanyar samar da muhimman bayanai ga hukumomin tsaron.

Kwankwaso ya kara da cewa a matsayin sa na tsohon ministan tsaro wanda kuma ya dade yana gwagwarmayar siyasa yayi imanin cewa magance matsalar tsaro hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnatin tarayya.

Ya ce dole ne ayi aiki tare don tabbatar da zaman lafiya a kasar nan.

Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kara da cewa mutane suna iya tuna lokacin da suke zuwa gona sabanin yanzu da ‘yan bindiga ke korar alumma daga kauyukan su.

Ya ce idan aka baiwa jam’iyar sa ta NNPP dama zata magance matsalar tsaro da sauran matsalolin da al’ummar kasar nan ke fuskanta.

Ya ce a yanzu NNPP ce mafita ga kasar nan tun da APC da PDP sun gaza fitar da kasar daga matsalolin da take ciki.

Ahmad Hamisu Gwale

Latest stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...

Related stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...