Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya isa jihar Lagos a wannan Lahadin domin gudanar da Sallar Idi karama ba bana.
A wasu hotuna da maitaimakawa shugaba Tinubu kan kafafan sada zumunta Dada Olusegun ya fitar a shafinsa na X ya ce tuni shugaban ya isa jihar tasa.
Olusegun ya ce Bola Tinubu ya samu tarba daga gwamnan jihar ta Lagos Babajide Sanwo-Olu da kuma Karin wasu jam’ian gwamnatin.
Dama dai mai bawa shugaban kasar shawara kan yada Labarai Ajuri Ngelale, a ranar Asabar ya sanar cewa Bola zai gudanar da Sallar Idi a jihar Lagos.
Ajuri Ngelale,ya kuma ce Tinubu zai bar Abuja zuwa Lagos domin gudanar da bukukuwan Salla karama da iyalansa, sai dai bai bayyana ko yaushe shugaban zai koma Abuja ba.
By Ahmad Hamisu Gwale