Saurari premier Radio
27.6 C
Kano
Tuesday, April 30, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTa'addanci ya karu a kasar nan saboda tasirin cin hanci da rashawa...

Ta’addanci ya karu a kasar nan saboda tasirin cin hanci da rashawa a tsakanin jami’an tsaro cewar gamayyar kungiyoyin arewacin kasar nan.

Date:

Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya “CNG” karkashin Dokta Nastura Ashir Sharif ta dira a Gusau babban birnin jihar Zamfara tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, biyo bayan sace daliban jami’ar tarayya ta Gusau da a ka yi kwanan nan.

Gamayyar kungiyoyin Arewar a ranar talatar da ta gabata ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da gwamnatin jihar Zamfara da su yi hakuri, su fuskanci kalubalen tsaro da kuma tabbatar da ganin an dawo da daliban jami’ar da aka sace.

Karamin ministan tsaro Muhammad Bello Matawalle yayi tir da sace dalibai mata na jami’ar tarayya dake Gusau a jihar Zamfara.

Har ila yau, gamayyar ta lura da cewa aiyukan ta’addanci sun ƙara ƙamari a sassan ƙasar nan, wanda hakan ke nuni da cewa cin hanci da rashawa yana kara tasiri a cikin jami’an tsaron.

Gamayyar kungiyar ta bayyana hakan ne a talatar da ta gabata lokacin da ta kai ziyara garin Gusau da nufin samar da hadin kai tsakanin gwamnatin Zamfara da hukumomin tarayya domin gudanar da ayyukan kawo karshen matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar da ma Arewa baki daya.

Da yake karin bayani ga jami’an gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan gwamnan jihar, kakakin gamayyar CNG, Abdul-Azeez Suleiman, ya ce al’amura a jihar Zamfara sun kara ta’azzara saboda rashin jituwar da ke tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara, wanda hakan ke haifar da zargi tsakanin bangarorin biyu.

A cewarsa, lamarin ya kara jefa jama’a cikin rudani da yiwuwar ta’azzara kalubalen tsaro a jihar.

Kungiyar ta ce abin takaici kan yadda aka gaza hada kai wajen magance matsalar tsaro, wanda har ta kai ga bangarorin biyu sun koma nuna yatsa ga juna. Ta ce wasan zargi kawai yana kawar da kai daga neman ingantattun hanyoyin magancewa da kuma zubar da amana da kwarin gwiwa da al’ummar Zamfara ke matukar bukata daga shugabanninsu.

Gamayyar kungiyoyin sun sami zarafin tattaunawa da karamin ministan tsaron kasar nan Bello Matawalle da Sarkin Gusau Alh. Ibrahim Bello da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Zamfara, Abdul’azeez Abdul’aziz Suleiman da shugaban jamai’ar tarayya ta Gusau, Farfesa Mu’azu Abubakar da sauransu.

Latest stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...

Related stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...