Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKwankwaso ya kware wajen yaudarar al'umma a cewar tsohon gwamna Ganduje.

Kwankwaso ya kware wajen yaudarar al’umma a cewar tsohon gwamna Ganduje.

Date:

Kwankwaso ya kware wajen yaudarar al’umma a cewar tsohon gwamna Ganduje.

Shugaban jam’iyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje, ya ce tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso zai cigaba da kasancewa mara nasara a siyasance.

Ganduje ya bayyana hakane a Larabar nan yayin da ya karbi tsohon dan takarar gwamna a jam’iyar NNPP a jihar Bauchi Haliru Dauda Jika wanda ya koma jam’iyar APC.

A cewar Ganduje son kai maimakon bukatun al’umma shine yake dakile buradin Kwankwaso na zama shugaban kasa.

Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana komawar Haliru Dauda Jika jam’iyar APC a matsayin abinda ya dace, yana mai cewa tsaya tsarin kwankwasiyya yaudara ce kawai.

Ya kara da cewa kungiyar kwankwasiyya da shugaban ta Rabi’u Musa Kwankwaso ya zama wajibi suyi hutun shekara takwas kafin sake dawowa gidan gwamnatin Kano.

Ganduje ya kara da cewa Kwankwaso ya kware wajen yaudarar al’umma.

Jam’iyar NNPP ta musanta dakatar da Kwankwaso

“Da yana PDP ya koma APC maimakon ya zauna amma sai ya fice ya koma PDP saboda ya gaza samun tikitin takarar shugaban kasa acan ma bai tsaya ba,” A cewar Ganduje.

Ya kara da cewa Rabi’u Musa Kwankwaso kwararrene wajen takarar shugaban kasa sannan zai cigaba da zama kwarare wajen yin rashin nasara. Domin kuwa yayi takarar shugaban kasa har sau biyu yana faduwa.

Da yake jawabi tsohon dan takarar gwamnan a jihar Bauchi karkashin NNPP ya ce ya koma APC ne saboda fatan da magoya bayan sa suke dashi na ganin komawar tasa.

Ya ce ficewar sa daga NNPP bata da alaka da Rabi’u Musa Kwankwaso.

Latest stories

Related stories