Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayya zata rabawa ‘yan Najeriya miliyan 62 tallafin kudi

Gwamnatin tarayya zata rabawa ‘yan Najeriya miliyan 62 tallafin kudi

Date:

Gwamnatin tarayya zata rabawa ‘yan Najeriya miliyan 62 tallafin kudi

Gwamnatin tarayya karkashin shugaba Bola Ahmad Tinubu ta ce zata fara tura kudi zuwa ga magidanta fiye da miliyan sittin daga watan Oktoba.

Ministar jinkai Betta Edu ce ta bayyana haka a hirar ta da gidan Talabijin na Arise ranar Litinin.

Tayi wannan jawabi yayin da take amsa tambayoyi kan halarta taron majalisar dinkin duniya karo na 78 da gwamnatin tarayya tayi.

Ta ce sun gana da bankin duniya kuma nan gaba kadan za a tallafawa magidanta dake tsananin bukata su miliyan 62 domin fara sana’o’in dogaro dakai.

Gobe litinin zamu fara rabon tallafin kayan abinci ga alummar jihar kano

Ta kara da cewa gwamnatin tarayya zata hada hannu da gwamnatocin jihohi da shugabanin al’umma a matakin kasa domin sanya mabukata cikin shirin rijitar wadanda zasu amfana da tallafin.

Betta Edu ta ce sun tura wakilai da suka gana da kungiyar gwamnonin kasar nan domin yin rijistar wadanda za a saka a tsarin tallafin na (National Social Register) kuma zasu fadada shirin.

Latest stories

Gwamnatin tarayya za ta sake bibiyar lasisin masu hakar ma’adana

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin ta na sake...

Hukumar Hisba ta jihar Kano zata aurar da ‘yan jarida 50

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu...

Related stories