Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJam'iyar NNPP ta musanta dakatar da Kwankwaso

Jam’iyar NNPP ta musanta dakatar da Kwankwaso

Date:

Jam’iyyar NNPP ta musanta labarin dakatar da madugun kwankwasiyya Rabi’u Musa Kwankwaso daga cikinta biyo bayan zargin yiwa jam’iyyar zagon kasa.

Da yake yiwa manema labarai jawabi a Yammacin yau shugaban jam’iyyar na jihar kano Hashimu Dungurawa yace NNPP bata da masaniyar wannan rahoto da ya bayyana matsayin marsas tushe da makama.

Yace yanzu haka masu ruwa da tsaki na gudanar da taron jam’iyyar a Abuja kuma babu abu mai kama da wannan da suke taattaunawa.

Hashimu Dungurawa ya bukaci al’uma suyi watsi da rahoton cewa an dakatar da tsohon dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso.

A kan wannan batu munyi yunkurin jin ta bakin shugaban NNPP din amma wayarsa bata tafiya.

Latest stories

Related stories