Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKaramin ministan tsaro Muhammad Bello Matawalle yayi tir da sace dalibai mata...

Karamin ministan tsaro Muhammad Bello Matawalle yayi tir da sace dalibai mata na jami’ar tarayya dake Gusau a jihar Zamfara.

Date:

Karamin ministan tsaro Muhammad Bello Matawalle yayi tir da sace dalibai mata na jami’ar tarayya dake Gusau a jihar Zamfara.
Matawalle wanda tsohon gwamnan jihar ta Zamfara ne yayin da yake Allah wadarai da sace daliban ya kuma jajantawa iyaye da al’ummar Zamfara kan sace daliban.
Wannan dai na cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar tsaro Attari M. Hope ya fitar a ranar Lahadi.
Matawalle ya bukaci hukumomin tsaro dasu rubanya kokarin su tare da amfani da kayan aiki wajen kubutar da daliban.
Gabanin fitar da sanarwar jajen al’umma a kasar nan sunyi ta sukar babban ministan tsaro Muhammad Badaru Abubakar da karamin ministan da ya fito daga jihar da aka sace daliban Muhammad Bello Matawalle bisa kin cewa ufan bayan faruwar lamarin.
Haka zalika ana alakanta sace daliban da sakacin hukumomi na rashin bada cikakken tsaro ga makarantun kasar nan da guraren kwanan dalibai.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...