Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumomin tsaro dasu gaggauta kubutar...

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumomin tsaro dasu gaggauta kubutar da daliban jami’ar tarayya ta Gusau mata da masu garkuwa da mutane suka sace a ranar Alhamis.

Date:

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumomin tsaro dasu gaggauta kubutar da daliban jami’ar tarayya ta Gusau mata da masu garkuwa da mutane suka sace a ranar Alhamis.
Mai taimakawa shugaban bangaren yada labarai Ajuri Ngelale, ne ya bayyana haka a ranar Lahadi a Abuja yayin da yake nuna takaicin sa kan sace daliban jami’ar.
Shugaban ya baiwa iyayen daliban da aka sace tabbacin cewa hukumomin tsaro zasu yi duk mai yiyuwa domin kubutar dasu.
Idan za a iya tunawa dai a daren ranar Alhamis din data gabata ne ‘yan bindiga suka farmaki gidajen kwana na dalibai dake wajen makaranta a Sabon Gida tare da sace dalibai mata masu yawan gaske saidai daga bisani wasu sun kubuto.

Latest stories

Related stories