Saurari premier Radio
33.4 C
Kano
Saturday, December 2, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJami’ar tarayya ta Nnamdi Azikiwe dake Anambra ta dakatar da malamai da...

Jami’ar tarayya ta Nnamdi Azikiwe dake Anambra ta dakatar da malamai da ma’aikatan da ba malamai ba guda 14 bisa zargin aikata laifuka daban daban ciki harda karbar kudi a hannun dalibai.

Date:

Jami’ar tarayya ta Nnamdi Azikiwe dake Anambra ta dakatar da malamai da ma’aikatan da ba malamai ba guda 14 bisa zargin aikata laifuka daban daban ciki harda karbar kudi a hannun dalibai.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jami’ar Dakta Emmanuel Ojukwu ya sanyawa hannu.
Cikin wadanda aka dakatar harda wanda ake zargi da kafe sunayen dalibai a matsayin wadanda suka fadi jarabawa duk da cewa sunyi nasara domin ya karbi kudi a hannun su.
Sanarwar ta kuma ce an dakatar da wasu dalibai tsahon shekarar daya tare da korar dalibi guda bisa samun su da laifin almundahana da damfara da kuma kin bada hadin kai yayin gudanar da bincike.

Latest stories

Related stories