Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu...

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnonin kasar nan da ministoci

Date:

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnonin kasar nan da ministoci su tabbatar cewa alumma sukewa shugabanta ba kawunan suba, domin acewarsa hakan ne kawai zai sa a samu zaman lafiya a nan gaba.
Tsohon shugaban kasa Buhari yace zarar matasa basu yadda da shugabanninsu ba kuma suna da dalilai na rashin yadda da shugabanninsu, to akwai matsala a nan gaba.
Buhari ya bayyana haka a tattaunawa da manema labarai kan cikar Najeriya shekaru 63 da samun yancin kai.
Tsohon shugaban kasa Buhari yace babban sakonsa ga yan kasar nan shine suyi hakuri da juna.

Buhari yace babban abinda ya haska yan Najeriya sun kara fahimtar siyasa inda suka ki zabar tsaffin gwamnoni 10 zuwa majalisar dattawa a zaben da ya gabata.

Buhari na wannan bayanai watanni kadan bayan kamma wa’adin mulkinsa na shekara 8, da ake ganin bayan saukarsa lamurran tattalin arzikin kasar nan na kara tabarbarewa.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...