Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSanyi: An samu gawar mata da miji a kulle a daki a...

Sanyi: An samu gawar mata da miji a kulle a daki a nan Kano.

Date:

An samu Sulaiman Idris, Dan shekara 28 da matar sa Maimuna Hallilu mai shekaru, 20 a mace a kan gadon su na aure.

 

Lamarin ya faru ne karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano a ranar Litinin.

 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Laraba.

Hatsari Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 20 A Jihar Oyo

Ya ce an gano ma’auratan basu fito daga dakin su ba tun a ranar Litinin da karfe 11 na safe.

 

Kiyawa, ya ce ofishin su dake kauyen Kwa a karamar hukumar Dawakin Tofa, ya karbi korafi a ranar Talata dake cewa wasu ma’aurata Sulaiman Idris da matar sa Maimuna basu fito daga dakin su ba tun ranar Litinin.

 

Bayan yin bincike an gano ma’auratan sun kunna gawayi don dumama dakin su saboda sanyi inda suka kulle suka kwanta bacci, Wanda hayakin gawayin yayi sanadiyar mutuwar su.

 

Ya kara da cewa yayin da kakar mijin ta tura kofar dakin ta same su yashe akan gado da kuma warin hayakin gawayin da ya cika dakin.

 

SP Kiyawa ya Kuma ce bayan samun rahoton ne jami’an su suka garzaya inda suka dauki gawarwakin zuwa asibitin Muratala inda a nan ne likita ya tabbatar da mutuwar su.

 

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce kwamishinan ‘yan sanda na Kano ya shawarci al’umma da su rinka lura wajen yin amfani da wuta a lokacin sanyi.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...