Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTsadar Mai: NMDPRA ta rufe gidajen Mai 14 a Kano

Tsadar Mai: NMDPRA ta rufe gidajen Mai 14 a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usmn

 

Hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa NMDPRA ta rufe gidajan Mai 14 a Kano da ke sayar da mai sama da farashin da ya kamata.

 

Jami’in hukumar a nan Kano Aliyu Muhammad Sama ne ya bayyana Hakan yayin kewayen da suka gudanar Alhamis dinnan.

 

Ya ce hukumar ta rufe gidajen man ne saboda siyarwa akan farashin N295 da kuma N300 Kan kowacce Lita.

 

“Muna da doka mai tsanani akan masu sayar da mai a sama da farashin gwamnati, da ta hadar da kwace lasisinsu, dakatar da su, ko kuma cinsu tara.

“Yanzu gidajen man da aka kulle za su biya tarar N150,000 kowannensu, kafin su ci gaba da sayar da man.

 

Ya ce manyan dillalan mai a yanzu na sayarwa akan N185, inda ya ce hukumar ta kulle gidajen Mai 120 a watan Disambar bara.

 

Ya ce duk gidan man da aka kama suna sayar da mai sama da farashin gwamnati to za dau mataki.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...