Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTinubu Na Ganawa Da Malaman Arewa Maso Yamma a Jihar Kano.

Tinubu Na Ganawa Da Malaman Arewa Maso Yamma a Jihar Kano.

Date:

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya na ganawa da Malaman addinin Musulunci na jihohin Arewa Maso Mammacin kasar nan.

 

Wakilinmu Ibrahim Hassan Hausawa ya rawaito cewa, an zabi jihar Kano ne domin gudanar da taron a yau, kuma wannan wani bangare ne na tattaunawa da masu ruwa da tsaki da Tinubun ke yi, gabanin babban zaben 2023.

 

Taron dai na gudana ne bisa jagorancin Nuhu Ribadu dake zama daraktan masu ruwa da tsaki, a tafiyar Tinubun.

 

Akwai malamai daga dariƙun Tijjaniyya, Izala, da Kadiriyya mutum 40 daga kowacce ɗarika, da suke hallaka a dakin taro na Amani dake unguwar Nassarawa GRA a Kano.

 

Gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar na daga cikin manyan mutanen da suka halarci wajen.

Latest stories

Related stories