Saurari premier Radio
26.4 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHatsari Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 20 A Jihar Oyo

Hatsari Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 20 A Jihar Oyo

Date:

Sama da fasinjoji 20 ne aka ruwaito sun kone kurmus yayin da wasu biyu suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a Lanlate, mahadar Maya a karamar hukumar Ibarapa ta Gabas a jihar Oyo.

 

Hadarin wanda ya hada da wata motar bas ta kasuwanci da wata mota kirar Sienna ya afku ne da yammacin ranar Juma’a.

 

Shaidu sun ce lamarin ya faru ne a sakamakon arangamar da ta yi sanadin barkewar gobara da ta cinye mutane sama da 20.

 

An kuma tattaro cewa fasinjoji biyu ne kawai suka tsira yayin da wasu kuma suka kone kurmus.

 

Shugaban karamar hukumar, Gbenga Obalowo wanda ya jagoranci tawagar masu Bada agajin gaggawa zuwa wurin ya bayyana abin a matsayin abin tausayi da takaici.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...