Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWani Dalibi Dan Nigeria Ya Bata A Kasar Cyprus

Wani Dalibi Dan Nigeria Ya Bata A Kasar Cyprus

Date:

Hukumar dake lura da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM) ta ce an samu rahoton bacewar wani dalibi dan Najeriya mai shekaru 28 a Arewacin Cyprus tun ranar 2 ga watan Agusta.

 

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai, Mista Abdur-Rahman Balogun ya fitar a Abuja.

 

Balogun ya ce mahaifiyar dalibin Hajiya Dije Ibraheem ce ta kai rahoton bacewar dalibin ga hukumar.

 

Rahoton dalibin da ya bace ya zo ne sa’o’i 24 bayan NiDCOM ta sake shawartar ‘yan Najeriya su guji zuwa yin karatu a Arewacin Cyprus.

 

Ya ce dalibin da ya bace, AbdulSamad Abubakar, ya kira mahaifiyar sa ne a ranar 2 ga watan Agusta, ta lambar wayar wani, yana kuka ya bayyana mata wasu da ba’a san ko su wanene ba sunzo su tafi dashi.

 

Hakan yasa ta kidime ta garzaya wajen kamfanin tafiye-tafiyen daya samar masa admission da takardun tafiya domin neman taimako amman ba su iya tallafa mata ba”

 

Balogun ya kara da cewar Mahaifiyar dalibin ta rubuta takardar koke ga ofishin jakadanci da shari’a na ma’aikatar harkokin wajen kasar, kafin ta zo neman sa hannun NiDCOM.

 

Sakataren Hukumar Sule Bassi ne ya karbi takardar koken a madadin Shugabar Hukumar NiDCOM, Misis Abike Dabiri-Erewa.

 

Inda ya tunatar da Mahaifiyar Abdulsamad, Hajiya Dije cewa harkokin diflomasiyya zai yi wahala, domin Najeriya da Majalisar Dinkin Duniya ba su da wata alaka ta diflomasiya da Arewacin Cyprus.

 

Sai dai ya ba ta tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da bincike tare da hadin gwiwar ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Ankara na kasar Turkiyya don gano danta a dawo da shi Najeriya.

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...