Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn Tsinci Gawar Wani Magidanci Bayan Shekaru Hudu Ana Neman Sa

An Tsinci Gawar Wani Magidanci Bayan Shekaru Hudu Ana Neman Sa

Date:

Rundunar ‘yan sanda a jihar Oyo ta tabbatar da samun gawar wani magidanci da aka shafe shekaru hudu ana neman sa.

 

Rundunar ‘Yan sandan ta ce hukumar binciken manyan laifuka ta jihar (CID) ta fara gudanar da binciken gawar wani aka gano a cikin dakin kwanansa da ke yankin Awotan, unguwar Apete a Ibadan.

 

A kwanakin baya wasu mazauna unguwar Awotan suka gano kwarangwal din mai gidan mai suna Aderemi Abiola a cikin dakin kwanansa bayan sun dauki tsawon lokaci suna nemansa.

 

Wasu masu aikin gayya a unguwar Awotan ne suka tsinci gawar mamacin bayan da suka nemi izinin ‘yansanda domin su kutsa kai cikin gidansa su sare ciyayun da suka tsiro a harabar gidan da ya shafe shekaru a rufe.

 

Yayin da suke aikin ne suka lura an bude taga daya daga cikin dakunan gidan Hakan yasa suk leka cikinsa, sai suka gano gawar mamacin manne akan gadon sa yana kwance.

 

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya tattaro daga mazauna yankin cewa an ga marigayin ne shekaru hudu da suka gabata.

 

Hakazalika marigayi Abiola ya kan zo Ibadan lokaci-lokaci daga Abuja kuma ba shi da wata alaka mai Karfi da makwabtan ta.

 

Da yake tsokaci akan lamarin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, SP Adewale Osifeso, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adebowale William, ya tura wata tawagar masu binciken laifuka zuwa gidan mamacin.

 

SP Osifeso ya ce kwamishinan ‘yan sandan ya kuma bayar da umarnin mika lamarin ga hukumar binciken manyan laifuka ta jihar (SCID), domin gano musabbabin mutuwarsa.

 

Kakakin ‘yan sandan ya ce yan uwan Marigayi sun tabbatar da rabon da su ga marigayin tun shekarar 2018, shekaru hudu da suka wuce.

 

A cewar Osifeso, kwamishinan ‘yan sandan ya yi kira ga jama’a masu kishin kasa da su taimaka wajen samar da bayanai masu amfani domin warware zare da abawa.

 

Ya Kuma bada tabbacin da zarar sun kammala bincike za su bayar da cikakkun bayanai ga alumma.

Latest stories

Related stories