Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Wednesday, April 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTa'addanci ne kamaTukur Mamu-Sheikh Gumi

Ta’addanci ne kamaTukur Mamu-Sheikh Gumi

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Fitaccen malamanin addinin nan da ke Kaduna Sheikh Ahmad Gumi ya ce ta’addanci babba kama Tukur Mamu.

 

A cewarsa ya kamata gwamnati ta gaggauta sakinsa ta kuma nemi yafiyarasa.

 

Tukur mamu wanda ke shiga tsakanin gwamnati da yan ta’adda ya fada komar jam’ian DSS ne cikin makon da ya gabata

 

Gumi na wannan furucin ne a karatunsa na mako-mako da ya saba gabatarwa a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

 

A cewarsa an cafke Mamu ne saboda rawar da yake takawa wajen kawo zaman lafiya a kasar nan.

 

Ya kara da cewa ko dai hukumar DSS ta sakeshi ko kuma ta gurfanar da shi a gaban kuliya.

 

A cewarsa, doka ta tanadi cewa ana gurfanar da duk wanda ake zargi a gaban kuliya bayan sa’a 24 da kama shi.

 

“Allah Yana jarabtar muminai, kuma wannan wata hanya ce ta jarrabawa daga Allah a kan Mamu.

 

“Ku kai shi kotu ya fuskanci shari’a don tsare shi a gidan yari ba tare da an bayyana laifinsa ba abun damuwa ne kwarai da gaske.

 

“Wannan lamari akwai firgici a cikinsa kuma ta’addanci ne.

 

Kama mutane bisa zalunci, shi ma ta’addanci ne; kamar yadda ’yan ta’addan ke yi ta hanyar zuwa gidan mutane su sace ko kuma su yi garkuwa da su.

 

“Ta ya za a yi mu ci gaba da rayuwa a irin wannan yanayi a karkashin gwamnatin da wa’adinta ya zo karshe?

“Babban fatanmu shi ne gwamnatin ta gama lafiya.

 

“Kuma ba wai don Tukur Mamu aka kama ba, kun san cewa duk wanda aka kama bisa zalunci sai na fito na yi magana, ballantana kuma a kama wanda na sani.

 

“Ina mai shawartar gwamnatin ta gaggauta sakinsa kuma ta nemi yafiyarsa komai ya zama tarihi,” a cewar Sheikh Gumi.

Latest stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Related stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...