Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Friday, March 29, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaGwamnatin Tarayya Zata Rufe Dakunan gwaje-gwajen Da Basu Da Rajista

Gwamnatin Tarayya Zata Rufe Dakunan gwaje-gwajen Da Basu Da Rajista

Date:

Gwamnatin tarayyar na shirin rufe dakunan gwaje-gwajen da ba a yiwa rajista ba a kasar don tsaftace fannin kiwon lafiya.

 

Karamin Ministan Lafiya, Joseph Ekumamankama ya bayyana haka yayin da ya bukaci mahukunta da ma’aikatan kungiyar kimiyyar dakin gwaje-gwajen lafiya ta Najeriya da kada su yi kasa a gwiwa wajen gudanar da ayyukansu bisa tsarin doka.

 

Ya yi wannan bayani ne a lokacin da mambobin ƙungiyar karkashin jagorancin magatakardar, Dokta Tosan Erhabor suka kai masa ziyarar ban girma a hedikwatar ma’aikatar lafiya da ke Abuja.

 

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta fitar a ranar Asabar ta hannun Daraktan yada labarai, Ahmed Chindaya, ministan ya bayyana cewa za a samar da tsare-tsare don tabbatar da gudanar da harkokin ƙungiyar cikin sauki.

 

Ya ce, idan akwai bukata, za a samar da tsare-tsare da za su taimaka wajen gudanar da ayyukansu, yadda ya kamata, domin cimma wa’adin da shugaban kasa ya dora a bangaren kiwon lafiya.

 

Ministan ya bada tabbacin asibitocin da ke karkashin ma’aikatar lafiya ta tarayya za su kasance farkon asibitocin da za su fara aiwatar da cikakken tanade-tanaden dokar, daganan kuma dakunan gwaje-gwaje a asibitocin jihar za su biyo baya. Da zarar an kammala hakan in ji ministan, za a rufe dakunan gwaje-gwajen likitocin da ba su yi rajista da MLSCN ba.

 

Latest stories

Related stories