24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiKwale-kwale ya halaka mata hudu da jaririya 'yar wata bakwai a Jigawa

Kwale-kwale ya halaka mata hudu da jaririya ‘yar wata bakwai a Jigawa

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Kwale-kwale ya halaka wasu mata hudu da jaririya ‘yar wata bakwai.

Rundunar  ‘yan sanda a jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wasu mata hudu da jaririya ‘yar wata bakwai bayan da kwale-kwale ya kife dasu a karamar hukumar Guri.

Mai magana da yawun rundunar DSP Lawan Shisu, ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce wadanda suka rasu sun hau kwale-kwale daga Nguru a jihar Yobe zuwa kauyen Adiyani na karamar hukumar Guri a jihar Jigawa.

An fara daukar sunayen malaman dake zuwa aiki a jami’ar Sule Lamido dake Jigawa

“Cikin rashin nasara kwale-kwalen ya kife dasu sai dai direban jirgin ya kubuta,” a cewar Shisu.

Ya ce bayan faruwar lamarin al’umma a yankin sun shiga ruwan don ceto mutanen saidai cikin rashin sa’a duk kansu sun mutu.

Shisu, ya ce tuni aka mika gawarwakin asibitin kauyen Adiyani, ya kara da cewa tuni aka fara gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar hatsarin.

Latest stories