Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Thursday, May 9, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoAkwai bukatar al'umma su dinga rijistar wadanda suka mutu a Kano -...

Akwai bukatar al’umma su dinga rijistar wadanda suka mutu a Kano – Hukumar kidaya.

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Hukumar kidaya ta kasa reshen jihar Kano ce ta fara kira ga alumma kan muhimmancin yin rijistar haihuwa da kuma ta wadanda suka mutu tsakanin alumma a sassan jihar nan.

 

Hukumar na wannan kirane a taron manema labarai da ta gudanar a nan Kano, a wani bangare na bikin da ta gudanar tun daga mataki na kasa kan muhimmancin adana bayanan wadanda aka Haifa da kuma wanda suka rigamu gidan gaskiya.

 

A taron da ya gudana a dakin taro na hukumar dake Kano, an zayyano irin tarin alfanu da yin rijistar haihuwa ke dashi tsakanin alumma.

 

Inda hakan ke taimakawa wurin kara karfafar bayanan da hukumar zata tura a yayin aikin kidaya da take jagoranta lokaci zuwa lokaci.

 

Dr. Isma’il Lawan Sulaiman babban kwamishinan hukumar kidaya a Kano, a yayin da yake jawabi a madadin shugaban hukumar kidaya ta kasa Nasir Isa Kwarra yace duk wanda bashi da sahihiyar rijistar haihuwa zai iya fuskantar kalubale na rasa katin zama dan kasa da kuma fasfo har ma da bias idan yana son zuwa kasashen ketare.

 

Dr. Isma’il Lawan Sulaiman ya kara da cewa babban dalilin da yasa a yanzu suke kara zaburar da jama’a kan yin rijistar haihuwa shine, domin idan sun gabatar da sakamakon kidaya na shekarar 2023 mai zuwa a amince da shi.

 

A nashi bangaran mai taimakawa gwamnan Kano kan sha’anin kidayar jamaa Malam Bashir Barwa yace gwamnatin Kano ta taimaka wurin samar da fassarar takaddara de ake daukar bayanai a harshen Hausa domin saukakawa alumma yin wannna rijista.

 

Dan Majen Kano kuma hakimin Gwale Alh. Yahya Inuwa Abbas da ya samu halattar wannan taro yace zasu cigaba da taimakawa a matsayinsu na iyayen kasa wurin ganin an tabbatar da alumma a Kano na yin rijistar haihuwa don dai jihar Kano ta cigaba da rike kambunta na jihar da ta fi kowacce yawa a fadin Najeriya.

 

Hakimin na Gwale yace Allah ya albarkaci jihar Kano da tarin jama’a don haka alumma su amsa kira dukkanin wadanda basu da rijistar haihuwa su tabbatar sunyi.

 

Dan Majen na Kano kuma hakimin Gwale Alh. Yahya Inuwa Abbas ya kuma bukaci alumma a duk sanda aka samu rashi, ya zama an shigar da bayanan mamacin ga hukumar ta kidayar jama’a ta kasa reshen jihar Kano duba da muhimmancin da wannan bayanai ke dashi ga hukuma wurin ayyukanta dama sauran ayyukan cigaban kasa.

Latest stories

Related stories