33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabarai'Yansanda sun kama Ibrahim Mamu a Masar

‘Yansanda sun kama Ibrahim Mamu a Masar

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

Jami’an tsaron a kasar Masar sun damke Ibrahim Mamu da ke shika tsakanin yan bindiga da iyalan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna tare da iyalansa.

 

An kama shi ne a hanyarsa ta tafiya kasar Saudiyya don gudanar da aikin Umrah yayinda aka tsareshi a tashar jirgin Alkahira na kwana guda.

 

Rahoton ya kara da cewa gwamnatin tarayya ce ta bukaci a damkeshi.

 

A hirar da akayi da shi, ya bayyana cewa bayan gudanar da bincike kansa da jami’an tsaron Masar sukayi, basu sameshi da wani lefi ba.

 

Mamu ya ce gwamnatin tarayya ta yi niyyar tsareshi kamar yadda aka yiwa mai rajin kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho, amma hakan bai yiwu ba saboda gwamnatin Masar ta tarar dukkan takardunsa sahihai ne.

 

Rahoton ya kara da cewa yanzu haka ana hanyar dawo da shi Najeriya.

Latest stories