Daga Mukhtar Yahya Usman
Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Bichi ta umarci kwamishinan yan sandan Kano ya binciki mawakiya Safara’u da Ado Gwanja da wasu mutum 7.
Wannan na kunshe cikin wata takarda da kotun ta fitar da ke dauke da kwanan watan 30 ga Agusta 2022.
Sauran wadanda za a tuhumar sun hadar da Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Dan Sarki, Murja Ibrahim, Ummi Shakira, Samha M Inuwa da kuma Babiyana.
Wannan dai ya biyo bayan korafin da wasu lauyoyi tara suka shigar kan a binciki mawakan.
Idan za a iya tunawa dai a baya bayan nan ne dai Ado Gwanja ya fitar da wata waka mai suna Asosa da ta yamutsa hazo.
Haka ma ita ma Safara’u ta fitar da wakoki da ake ganin ba dai dai bane ga tarbiyyar Addini.