33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGwamnati ta kafa kwamiti don sake nazartar bukatun ASUU

Gwamnati ta kafa kwamiti don sake nazartar bukatun ASUU

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamiti don sake duba bukatun kungiyar ASUU

 

Kungiyar ta tsunduma yajin aiki ne a watan Fabrairu saboda wasu bukatu.

Bukatun sun Hadar da inganta jami’o’in, da sabon tsarin biyan malaman jami’a na UTAS, da sauransu.

Tuni dai gwamnati ta daina biyan malaman albashi, tana mai cewa bai kamata a biya su ba tunda ba su yi aiki ba, kuma ba za a biya su watannin da suka shafe suna yajin aikin ba.

Matakin ya kara harzuka malaman jami’ar.

To amma a zaman da gwamnatin ta yi da iyaye da shugabannin jami’o’i mallakar gwamnatin tarayya ranar Talata, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya ce gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti domin sake duba batun.

Malam Adamu Adamu ya ce kwamitin zai kunshi iyayen jami’o’i hudu, da shugabannin jami’o’i hudu a yayin da shi kuma zai jagoranci

Latest stories