Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn fara daukar sunayen malaman dake zuwa aiki a jami'ar Sule Lamido...

An fara daukar sunayen malaman dake zuwa aiki a jami’ar Sule Lamido dake Jigawa

Date:

Muhammad Bello Dabai

 

Jami’ar Sule Lamido dake Kafin Hausa a jihar Jigawa ta umarci malaman dake koyarwa a jami’ar da su koma bakin aiki.

 

Wannan matakin na zuwane bayan taron gaggawa da hukumar gudanarwar jami’ar ta gudanar karo na 30.

 

A sanarwar da sakataren jami’ar Malam Adamu Mohammed ya fitar, tace tuni jami’ar ta umarci shugabannin sassanta da fara daukar sunayen malaman da suka koma aiki daga jiya litinin zuwa 5 ga watan gobe.

 

Wannan mataki da jami’ar ta dauka baya rasa nasaba da gaza cimma matsaya tsakanin kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU da gwamnatin tarayya kan yajin aiki da aka kwashe sama da rabin shekara anayi.

 

To sai dai ana ganin akwai kalubale da jami’o’in na gwamnatocin jihohi zasu iya fuskanta, duba da akwai malaman jami’o’i mallakin gwamnatin tarayya masu yawa da sune suke koyarwa a jami’o’in mallakin jihohi

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...