Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnatin Kano ta jajantawa alummar jihar kan ambaliyar ruwa.

Gwamnatin Kano ta jajantawa alummar jihar kan ambaliyar ruwa.

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Gwamnatin Kano ta mika sakon jaje ga alummar jihar Kano wadanda iftila’in ambaliya ruwa ya shafa a jihar.

 

Gwamnatin tace ta fara nazarin matsalar ambaliyar kuma ta kafa wani kwamiti da zaiyi aiki cikin gaggawa kan ambaliyar da ake samu a baya-bayannan a jihar Kano.

 

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano Muhammad Garba ya fitar ya ce kwamitin da aka kafa zaiyi duba kan tituna da magudanan ruwa da suka toshe ko suka lalace, domin tabbar da an gina sabbi tare da gyara wadanda suke bukatar gyara.

 

Haka kuma za’a rushe gine-gine da akayi kan magudanan ruwa a sassan jihar.

 

Mamakon ruwan sama da ake samu a yan kwanakin nan ya jefa fargaba a zukatan alumma a Kano, bayan ambaliya da aka fuskanta a wasu sassan kwaryar birnin Kano ciki har da babbar kasuwar nan ta kayan sawa wato Kwari.

 

Masu bibiyar lamurra dai sun fara kira ga alumma dasu tashi tsaye don gyara magudanan ruwa a jihar domin kaucewa faruwar ambaliya da zata kawo barazana ga jama’a.

 

Latest stories

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa...

Related stories

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa...