24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGanduje ya jajantawa wadanda rugujewar gini ta shafa a kasuwar saida wayoyi...

Ganduje ya jajantawa wadanda rugujewar gini ta shafa a kasuwar saida wayoyi ta Beirut

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Gwamnan Kano Ganduje, ya dage rantsar da sabin kwamishinoni a Larabar nan tare da jajantawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa da wadanda gini ya fado musu a kasuwar saida wayoyi ta Beirut.

 

Cikin sanarwar da kwamishinan yada labarai Muhammad Garba, ya fitar gwamna Abdullahi Umar Gamduje, ya jajantawa wadanda al’amarin ya shafa tare da bada umarnin ci gaba da bincike don kubutar da wadanda suka makale a ginin da ya rushe.

 

Ya bada tabbacin ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin rugujewar ginin yayin da ake tsakiyar ginawa.

‘Yan sanda a Kebbi sun kama matar da ta kashe mijinta

 

Cikin sanarwar Ganduje ya kuma yi alhini ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a sassa daban daban na jihar nan.

Latest stories