33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiMatan Kano sun karrama Atiku Abubakar da Ludayi

Matan Kano sun karrama Atiku Abubakar da Ludayi

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

Matan jam’iyyar PDP a Kano karkashin jagorancin sanata Baraka Sani sun karrama Alhaji Atiku Abubakar da katon ludayi.

 

A jawabinta sanata Baraka ta ce sun karrama shi da Ludayin da suka yiwa lakabi da na ‘Diban Romon Demokradiyya’ ne saboda cancantarsa.

 

Baraka ta ce mata su ne kashin bayan Demokradiyya don haka dole ne suma a basu damarsu don a dama da su.

 

Ya kuma bukaci dukkanin matan da ke jihar Kano su fito kwansu da kwarkwata domin su zabi Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa shekara mai zuwa.

 

Ta ce matan Kano ba za su yi nadama ko da na sani ba idan suka zabeshi.

 

A nasa jawabin Alhaji Atiku Abubakar ya godewa matan da suka taru don karramashi.

 

Ya ce ko Kadan ba zai basu kunya ba kuma zai Sanya bukatunsu a gaba da zarar ya zama shugaban kasa.

Latest stories