Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Kano ta kulla yarjejeniya da gidauniyar Aliko Dangote don magance cutar...

Gwamnatin Kano ta kulla yarjejeniya da gidauniyar Aliko Dangote don magance cutar Tamowa

Date:

Gwamnatin Kano ta sanya hannu da gidauniyar Aliko Dangote, a wata yarjejeniyar hadin gwiwa don magance matsalar tamowa ga kananan yara.

 

Kwamishinan lafiya na jihar nan Aminu Ibrahim Tsanyawa, ne ya jagiranci sanya hannun a Larabar nan.

 

Wadanda suka sanya hannu a yarjejeniyar sun hada gidauniyar Aliko Dangote, data Bill And Milinda Gates da kuma hukumar lura da kananan yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) da gwamnatin jihar Kano.

 

Cikin yarjejeniyar duka bangarorin hudu zasu rinka sanya naira miliyan dari da tamainin da biyar (185) domin yaki da cutar a jihar Kano.

Da take jawabi shugabar gidauniyar Aliko Dangote, Hajiya Zuwaira Yusuf, ta ce akwai iyaye da yawa a jihar nan da basa iya samarwa da ‘ya’yan su kanana abinci mai gina jiki wanda hakan yasa suka sake kulla yarjejeniyar domin zakule matan dake tare da yaran dake fama da cutar tamowa tare da basu kulawar data dace.

 

Ta ce bayan aikin cutar shan inna sai suka lura yara da yawa musamman a karkara na fama da cutar tamowa.

Jihar Kano za ta Kaddamar da shirin kare Lafiyar iyaye mata da Jarirai.

Ta kara da cewa za kuma a koyawa iyaye mata yadda zasu rinka hadawa ‘ya’yan su abinci mai gina jiki don kare su daga cutar tamowa.

 

A nasa bangaren kwamishinan lafiya na jihar Kano Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya ce gwamnatin Kano ta shiga ‘yarjejeniyar ne don ci gaba da inganta lafiyar al’ummar jihar nan.

 

Ya kara da cewa gwamnati zata cigaba da hada kai da kungiyoyi irin wadannan don ciyar da bangaren lafiya gaba.

 

 

Latest stories

Related stories