Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJihar Kano za ta Kaddamar da shirin kare Lafiyar iyaye mata da...

Jihar Kano za ta Kaddamar da shirin kare Lafiyar iyaye mata da Jarirai.

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Gwamnatin Kano za ta kaddamar da wani gawurtaccen shirin kare lafiyar iyaye mata da jarirai, wanda ya hada da samar da abinci mai gina jiki.

Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da kwararraru kan kiwon lafiyar al’umma ke nanata muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zalla a watanni shida na farkon haihuwar su.

Wata kididdiga da hukumar lafiya ta duniya ta fitar ta nuna cewa, Najeriya na da kaso 30 na adadin matan dake mutuwa yayin haihuwa da mace-macen jarirai a duniya.

Haka kuma kididdigar ta nuna cewa jihar Kano na cikin jihohin dake kan gaba wajen fuskantar wannan matsala.

Sai dai ga alama hukumomin jihar sun himmatu wajen daukar matakan dakile wannan matsala, la’akari da yunkurin gwamnatin jihar na samar da wani daftarin bayanai da ka’idojin samar da abinci mai gina jikin jarirai da mata masu juna biyu.

Hajiya Halima Musa Yakasai dake zaman daraktar kula da ingancin abinci a ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce shiri ne na gwamnatin tarayya, wanda aka kaddamar da shi a shekara ta 2018, kana daga bisani aka umarci jihohi 36 na kasar nan su kaddamar da shi su ma.

A cewar, Dr Ashiru Hamza Mohammed Kodinetan shirin bunkasa lafiyar jarirai da mata masu juna biyu wato Alive & Thrive, ya ce akwai bukatar daukar matakan wayar da kan jama’a game da muhimmacin samar da cimaka ga mata da yara, musamman masu juna biyu da kuma jarirai.

Yanzu haka dai gwamnatin jihar Kano na kuma tsare-tsaren kafa cibiyar kula da yara masu fama da cutar Tamowa, yayin da a hannu guda kuma kwararru kan kiwon lafiya ke jan hankalin hukumomin kan yadda ake shigo da magungunan sanya jarirai kuzari barkatai cikin kasar nan.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...