Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNan gaba kadan zan bayyana makomata a NNPP- Shekarau

Nan gaba kadan zan bayyana makomata a NNPP- Shekarau

Date:

Ahmad Hamisu Gwale

Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, ya musanta labarin cewa a anar Litinin dinnan zai fice daga jamiíyyar NNPP zuwa PDP kamar yadda wasu ke ta yadawa.

Sanata Shekarau ya bayyana haka ne  ranar Litinin a taron manema labarai da ya gudanar a gidansa da ke Mundubawa.

“Har yanzu ina nan a NNPP, amma  yadda ake ci gaba da samun rashin adalci da kuma rashin cika alkawarin da aka kulla da alamu nan gaba kadan zan bayyana matsaya ta karshe kan batun zama ko kuma ficewa daga NNPP”

Malam Ibrahim shekarau ya kuma ce shakka babu jami’iyyu daban-daban sunyi zawarcinsa, domin ya yi musu takarar mataimakin dan takarar shugaban kasa, amma bai aminta da tayin da akai ma sa ba.

Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da suyi hakurin kammala jiran rahotan karshe na shugabancin kwamitin shura, wanda dama sune ke nuna inda alkibilarsa a siyasance ke kasan cewa.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories