Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Tuesday, April 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiManchester United ta doke Liverpool da ci 2-1

Manchester United ta doke Liverpool da ci 2-1

Date:

Daga Ahmad Hamisu Gwale

 

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta doke abokiyar hamayyarta Livepool da ci 2-1 a wasan da suka fafata a ranar Litinin.

 

Manchester United da Liverpool na hammaya da juna, inda suka fafata a filin Old Trafford wasan da ya dauki hankalin al’umma da dama a fadin duniya.

 

Dan wasa Jadon Sancho ne ya fara zura kwallon farko a minti na 16, bayan samun tai mako daga hannun Anthony Elanga.

 

Sai kuma dan wasa Marcus Rashford da shima ya zura kwallonsa a minti na 53 bayan samun tai mako daga Anthony Martial.

 

Alkalin wasa Michael Oliver dan kasar Ingila ne ya karbi bakuncin wasan da shine karo na 210 da kungiyoyin suka buga tsakaninsu a gasar Firimiya.

 

Inda Liverpool tayi nasara a wasanni 70, sai Manchester United tayi nasarar wasanni 82 jumulla harda na wannan rana.

 

Sai kuma aka tashi canjaras a wasanni 58, a duka wasannin da manyan kungiyoyin kasar biyu Ingila suka buga.

 

Kafin fara wasan dai an gabatar da sabon dan wasan da United ta siya Casemiro daga Real Madrid.

 

Wanda ya nuna farin cikinsa da kasancewarsa a kungiyar dad an wasan ya bayyana yana fatan zai lashe kofina da dama.

 

Yanzu haka dai Manchester United ta samu nasara a karon farko a gasar Fimiyar bana, wanda hakan ya bata damar komawa mataki na 14 da maki uku jumulla.

 

Yayinda Liverpool kuwa ke mataki na 16 da maki biyu a wasanni ukun data buga a sabuwar gasar Firimiyar shekarar 2022/2023.

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...